in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin kan batun Syria ya jaddada bukatar komawa teburin shawarwari
2017-04-24 10:20:53 cri
Wakilin musamman na Sin game da batun kasar Syria, Xie Xiaoyan, ya jaddada bukatar sake komawa teburin shawarwari, matakin da a cewarsa shi ne kawai zai bada damar kawo karshen matsalar da kasar Syria ke fama da ita a yanzu haka.

Da yake zantawa da manema labaru na Sin da na Masar a birnin Alkahira a jiya Lahadi, Mr. Xie ya ce bai ga wata hanya ta gaggawa da za ta kai ga warware rikicin kasar Syria ba, kuma tabbas daukar matakan soji ba za su haifar da mai ido ba.

Ya ce Masar jigo ce a fannin warware matsalolin kasar Syria, tana kuma hadin gwiwa da Sin a wannan fanni mai matukar muhimmanci. Kaza lika ya ja hankalin masu ruwa da tsaki game da girman kalubalen da ake fuskanta, yana mai cewa yanayi a Syria na kara tsananta, duba da yadda aka samu aukuwar harin makamai masu guba a kasar a kwanakin baya.

Game da matsayar Sin kan hakan, Mr. Xie ya ce kasarsa na adawa da amfani da makamai masu guba ta kowace irin fuska, kuma Sin na fatan za a gudanar da bincike mai zaman kansa bisa kwarewa, domin hukunta wadanda suka aikata wannan ta'asa.

Xie Xiaoyan na ziyarar aiki ne a Masar, inda tuni ya gana da jami'an ma'aikatar harkokin wajen kasar, a wani yunkuri na zakulo hanyoyin warware batun Syria ta hanyar lumana. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China