Bugu da kari, Sean Spicer bai kawar da yiyuwar sake harba mamakamai masu linzami kan dakarun sojin gwamnatin Syria bisa umurnin shugaba Donald Trump ba. Ya kara da bayyana cewa, idan an sake yin amfani da makamai masu guba ko boma-boman man fetur kan fararen hula a kasar Syria, tabbas kasar Amurka za ta mayar da martani. (Sanusi Chen)