in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron Amurka: yawan jiragen saman yaki na Syria ya ragu da 20%
2017-04-11 10:31:54 cri
A jiya Litinin, ministan tsaron kasar Amurka James Mattis ya ce, bayan da rundunar sojan kasar Amurka ta jefa makamai masu linzami a filin jiragen saman yaki na Shayrat dake yankin tsakiyar kasar Syria a ranar 6 ga wata, yawan jiragen saman yaki na kasar Syriyar ya ragu da kashi 20 cikin dari.

Mr. Mattis ya kara da cewa, wuraren adanar man fetur dake wannan filin jiragen saman yaki da karfin dakile hari daga sama na wannan fili dukkasu sun lalace. Ya kuma bayyana cewa, yanzu gwamnatin kasar Syria ba za ta iya ci gaba da yin amfani da wannan filin jiragen saman yakin wajen samar da makamashi ga jiragen saman yaki ko samar da kayayyakin soja ba.

Mr. Mattis ya kuma bayyana cewa, wannan matakin harba makamai masu linzami a filin matakin mayar da martani ne na taka tsantsan da gwamnatin kasar Amurka ta dauka ga lamarin da aka yi amfani da makamai masu guba a kasar Syria a ran 4 ga wata, domin kokarin hana sake yin amfani da makamai masu guba a kasar Syria a nan gaba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China