A cikin sanarwar da ta fitar, gwamnatin kasar Bahrain ta ce, kasar Qatar tana tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Bahrain, baya ga goyon bayan ayyukan ta'addanci. Sakamakon haka, kasar Bahrain ta tsai da kudurin yanke huldar diflomasiyya dake tsakaninta da kasar Qatar, kana ta dawo da ma'aikantan diflomasiyyar dake kasar Qatar, Sannan ta umarci ma'aikatan diflomasiyya na kasar Qatar dake kasar Bahrain da su kwashe ya nasu ya nasu su bar kasar cikin sa'o'i 48. (Sanusi Chen)