Wang wanda ya bayyana haka a jawabinsa yayin babban taro kan tsaro karo na 53 da aka fara jiya Jumma'a a birnin Munich, ya ce muhimman batutuwan da taron ya ba muhimmanci sun hada da tattauna muhimman batutuwa kan tsaro, ciki har da kawancen kasashen yankin tekun Atlantika da dangantakar kasashen Yamma.
Ministan ya ce har yanzu, tabbatar da tsaro da samar da ci gaba, su ne muhimman batutuwa da aka sanya gaba a duniya.
Har ila yau, Wang Yi ya ce manyan kasashe na da dimbin arziki da damarmaki, don haka, suna da muhimmiyar rawar takawa wajen tabbatar da tsaro da wanzar da zaman lafiya a duniya tare da bada gudunmuwa ga ciyar da al'umma gaba. ( Fa'iza Mustapha)