Wang Yi ya bayyana haka ne a jawabinsa, yayin babban taro kan tsaro da aka fara jiya Jumma'a a birnin Munich.
Yayin taron za a tattauna muhimman batutuwa kan tsaro, ciki har da kawancen kasashen yankin tekun Atlantika da dangantakar kasashen Yamma.
Ministan ya ce, cikin wasu muhimman jawabai biyu da ya yi a Switzerland cikin watan da ya gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da gina al'ummu ta yadda za a samu ci gaba da makoma mai kyau na bai daya.
Ya ce tabbatar da tsaro da samar da ci gaba, su ne muhimman batutuwa da aka sanya gaba a duniya.
Har ila yau, Wang Yi ya ce bai kamata hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama ya zama tsohon batu ba, a don haka ya kamata a inganta shi tare da sake karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe. ( Fa'iza Mustapha)