A lokacin da majalisar Amurka ke yin zama don tantance shi, Branstad ya ce, a matsayinsa na gwamnan jihar Iowa yana ganin alamu na samun kyakkyawar dangantakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Ya ce idan har aka tabbatar da shi a wannan mukami, zai yi aiki tukuru wajen samar da kyakkyawan tasiri na karfafa dangantaka tsakanin Amurka da Sin.
Branstad ya fadawa 'yan majalisar Amurka cewa bangaren harkokin sufurin jiragen sama, da samar da kayayyaki a masana'antu, da sinadarai, da na'urorin lantarki, da sauran kayayyaki da ayyuka na musamman ne ake fitar da su zuwa kasar Sin a kowace rana wadanda suke matukar tallafawa ci gaban tattalin arzikin Amurka.
Sannan ya bayyana dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin da cewa dangantaka ce ta fuskoki da dama, Branstad ya kuma lura cewa dole ne kasashen biyu su yi aiki tare wajen muhimman ayyuka da suka shafi batun tsaro, ciki har da batun dakile shirin kera makaman nukiliyar Korea ta arewa da kuma tabbatar da tsaro wajen yaki da masu yin kutse ta hanyar yanar gizo.
Branstad ya kara da cewa, zai yi kokari matuka wajen ci gaba da wanzuwar musayar al'adu da fasahohi da al'ummar Sinawa. (Ahmad Fagam)