in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya yi kira da kara tabbatar da hadin kai tsakanin kasashe
2017-02-18 17:25:43 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi kira ga kasashe a fadin duniya su hada kai tare da daukan matakai da suka dace.

Wang Yi ya bayyana haka ne a jawabinsa, yayin babban taro kan tsaro karo na 53 da aka bude jiya Juma'a a birnin Munich na kasar Jamus.

Ministan ya ce, cikin wasu muhimman jawabai biyu da ya yi a Switzerland cikin watan da ya gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da gina al'ummomi ta yadda za a samu ci gaba da makoma mai kyau na bai daya.

Ya ce akwai bukatar tabbatar da hadin kai, wanda ya bayyana a matsayin hanyar wanzar da zaman lafiya da samun bunkasa da warware matsalolin da suka addabi duniya.

Har ila yau, Wang Yi ya ce, bai kamata hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama ya zama tsohon batu ba, a don haka ya kamata a inganta shi tare da sake karfafa hadin gwiwa tsakanin manyan kasashe. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China