Jakada Cui wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, ya ce ko da har yanzu Trump bai yi magana game da manufar gwamnatinsa a kan kasar Sin ba, da alamun dangantakar kasashen biyu kamar yadda aka saba ba za ta canja ba.
Jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, dangantakar kasashen biyu ta dace da moriyarsu, kasancewarsu manyan kasashen masu karfin tattalin arziki a duniya, kana kasashe masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na MDD.
Ya kuma bayyana fatan cewa, bangarorin biyu za su ci gaba da rumgumar matakan tattaunawa da yin musaya kamar yadda suka saba yi a shekarun baya.
Cui Tiankai ya ce matakan da kasashen biyu suka dauka na gina sabuwar dangantakar abokantaka ta rashin takalar juna da mutunta juna da hadin gwiwar moriyar juna sun kai ga cimma gagarumar nasara. (Ibrahim Yaya)