Bankin tsakiya na Sin ya bayyana adadin musayar kudaden da aka adana bisa ma'aunin SDR karo na farko
Bankin jama'ar kasar Sin ya gabatar da yawan musayar kudi da kasar ta ajiye bisa ma'aunin dalar Amurka a ranar 7 ga wata, kana a karo na farko ya gabatar da yawan musayar kudi da aka adana bisa ma'aunin SDR. Bisa kididdigar da bankin ya yi, yawan musayar kudade da suka rage na ajiya a kasar Sin a watan Maris ya kai dala biliyan 3210, wato biliyan 2280 bisa ma'aunin SDR.
SDR shi ne ma'aunin abin da aka ajiye da asusun bada lamuni na duniya ya kafa a shekarar 1969, wanda yake da kima kamar irin su zinare da musayar kudade aka adana a duniya.
Bankin tsakiya na kasar Sin ya yi hakan ne, don sassauta tasirin da dalar Amurka ta yiwa darajar kudin Sin RMB da ta musayar kudade da Sin ta ajiye, da magance dogaro kan kudi irin daya kawai. (Zainab)