Kakakin masu sintirin tsaron Ayob Qassem shi ne ya bayyana haka a yayin taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, inda ya cewa, wadannan bakin haure da suka hada da mata 27 da yara 8, yawancinsu sun fito daga kasashen Syria, Masar, Ghana da dai sauransu. Da ma sun yi niyyar satar shiga Turai ta jiragen ruwa, amma sai suka gamu da matsalar jirgin ruwa, daga baya kuma masu tsaron gabar teku suka gano su. Baya ga haka, kakakin ya bayyana cewa, za a kai wadannan bakin haure da suka shigo yankin ba tare da izni ba zuwa cibiyar kula da bakin haure dake yammacin kasar ta Libya, kafin a mayar da su kasashen su. (Bilkisu)