in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kula da 'yan gudun Hijira ta MDD za ta inganta ayyukan agaji a Libya
2017-05-22 09:57:03 cri
Shugaban hukumar kula da 'yan gudun Hijira ta MDD Flippo Grandi, ya ce hukumar za ta kara inganta ayyukanta a Libya domin taimakawa kasar magance al'amura dake kara rikicewa.

Flippo Grandi ya bayyana haka ne a jiya, lokacin da ya kai ziyara Tripoli babban birnin Libya, inda ya hadu da 'yan gudun hijira da 'yan ci rani a wasu cibiyoyin tsugunar da 'yan gudun hijira.

Ya ce ya kadu matuka da yanayin da ya tsinci 'yan ci rani da 'yan gudun hijira a ciki, saboda rashin kudi. Inda ya ce bai kamata mata da yara da maza da suka sha bakar wuya, su ci gaba da jure irin wannan wahala ba.

Ya ce ya kamata mu mai da hankali kan kalubalolin da za a fuskanta a yayin da ake aiki a waje kamar Libya mai fama da rikici muhimmanci. Inda ya kara da cewa, iya kai dauki da ba da kariya da ake bukata kalubale ne na dindindin.

Jami'in ya ce mutanen da suke son a ba su taimako da ma'aikatan UNHCR wadanda suke da rayuwa da aiki a wurin suna cikin hatsari sosai.

A cewar hukumar UNHCR, kimanin al'ummar Libya 300,000 ne rikici da ake yi a kasar, ya raba da matsugunansu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China