Uhuru Kenyatta wanda ya jagoranci bikin ranar Ma'aikata ta duniya jiya a binrin Nairobi, ya ce ya yi karin ne domin ragewa kananan ma'aikata radadin da suke fuskanta.
Shugaba Kenyatta ya kuma ba da umarnin kara alawaus-alawus mara haraji da kudin aikin da baya cikin lokaci zuwa dala 1,000 domin taimakawa kananan ma'aikata.
Ya ce ya fahimci cewa, ma'aikata na bukutar karin kudin shiga domin sauke nauyin bukatun iyalansu, inda ya ce ba a yi musu adalci ba wajen kakaba musu haraji mai yawa.
Shugaba Kenyatta ya umarci sakataren fadarsa kan harkokin masana'antu Adnan Mohammed ya gaggauta kiran taro da ma'aikata domin lalubo matakan ragewa kananan ma'aikatan radadin tsadar kayyaki. (Fa'iza Mustapha)