Uhuru Kenyatta ya yi kira ga hukumomin tsaro su samar da wasu dabaru da za a rika amfani da su tsakanin hukumomin daban-daban, wanda ya ce ya taimakawa kasar ganowa tare da datse hanyoyin sadarwa tsakanin 'yan ta'adda.
Ya ce tilas ne hukumomin tsaro su dai na amfani da tsarin nan na kin musayar bayanai, tun da ya gaza haifar da mai ido.
Shugaban kasar ya yi bayanin cewa, hadin gwiwa tsakanin hukumomin sabanin tsarin na kin musayar bayanai, ya cimma nasarori wajen ganowa da karewa da kuma datse manufofi da ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda.
Shugaban na wannan bayani ne yayin yaye kashi na 19 na manyan jami'an soji. Wannan shi ne karon farko da shugaban kasar ya yi jawabi ga jami'an tsaro dake karbar horo a kwalejin horas da sojoji. (Fa'iza Mustapha)