in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Kenya ta yi gargadin yiwuwar kai harin ta'addanci a Mombasa
2017-05-26 09:43:06 cri
Mahukuntan kasar Kenya sun yi gargadin cewa, akwai yiwuwar kungiyar Al-Shabaab za ta kai harin ta'addanci birnin Mombasa dake gabar ruwa a cikin watan Ramadan.

Kwamishinan yankin Mombasa Evans Achoki ya bayyana cewa, yanzu haka an girke jami'an 'yan sanda a sassa daban-daban na birnin don ganin an kawar da duk wata barazanar ayyukan ta'addanci a yankin.

Ya ce, duk da cewa jami'an tsaro sun yi nasarar rage karfin kungiyar ta Al-Shabaab a birnin, amma ya bukaci mazauna yankin, da su rika sanya ido tare da sanar da hukumomi muhimman bayanai.

A karshen mako ne al'ummar musulmi a fadin duniya za su fara Azumin watan Ramadan, kamar yadda aka umarci Annabi Muhammadu a cikin Alkura'ani.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China