Rundunar 'yan sandan jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya, ta tabbatar da mutuwar 'yan gudun hijira hudu, sanadiyyar wani farmaki da kungiyar Boko Haram ta kai musu a ranar Asabar da ta gabata.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Damian Chukwu, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a jiya cewa, wadanda al'amarin ya rutsa da su mafarauta ne, kuma 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne suka musu kwantan bauna da yammacin ranar Asabar, a lokacin da suka bar sansaninsu dake birnin Maiduguri don farauta a daji.
Jami'in ya kuma ayyana batan wani dan gudun hijira guda dake tare da mafarautan.
Damian Chukwu ya ce, ana gudanar da bincike kan harin, yana mai cewa, tuni aka sanar da rundunar soji game da al'amarin.
Wannan irin kisa dai ita ce ta farko da aka taba samu tun bayan bude sansanonin 'yan gudun hijira a Maiduguri. (Fa'iza Mustapha)