Hukumar 'yan sanda a Najeriya ta tabbatar da cewa, mata 3 'yan kunar bakin wake sun hallaka kansu bayan wani harin da suka yi niyyar kaddamarwa wanda bai samu nasara ba a wani kauyen dake kusa da birnin Maiduguri a arewacin kasar.
Maharan sun tayar da boma bomai ne dake daure a jikinsu, inda suka kashe kansu su kadai, bayan da jami'an tsaro suka gan su, in ji Victor Isuku, kakakin hukumar 'yan sanda.
Isuku ya shedawa 'yan jaridu cewa, maharan sun yi yunkurin kaddamar da harin ne a kauyen Mamanti a yankin Molai na birnin Maiduguri.
Hare haren ta'addaci na 'ya'yan kungiyar Boko Haram, sun yi sanadiyyar hallaka rayukan dubban jama'a, kana sun raba wasu mutanen miliyan 2.3 da muhallansu, tun bayan barkewar rikicin a shekarar 2009.
Maiduguri, ta jihar Bornon dake arewa maso gabashin Najeriya ta kasance babbar helkwatar mayakan, kafin daga bisani dakarun Najeriya suka fatattaki mayakan na Boko Haram daga babbar maboyarsu dake dajin Sambisa a watan Disamba.
Sojojin Najeriya suna ci gaba da yin sintiri babu kakkautawa a yankin.(Ahmad Fagam)