in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNDP da Sudan sun rattaba hannu kan yaki da tsattsauran ra'ayi
2017-05-30 12:34:09 cri
Gwamnatin kasar Sudan ta ce ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninta da shirin raya kasashe na MDD kan hadin gwiwa wajen yaki da akidar tsattsauran ra'ayi.

Sanarwar da hukumar yaki da ayyukan ta'addanci ta kasar (SNCCT) ta fitar, ta ce yarjejeniyar na da nufin kare matasa da mutanen da ke cikin hadarin fadawa akidar tsattsauran ra'ayi da kuma karfafa ayyukan kungiyoyin al'umma a matakin kasa da jihohi wajen magancewa tare da dakile akidar tsattsauran ra'ayi a Sudan.

Sanarwar ta kuma ruwaito cewa, za a shafe tsawon shekaru 3 ana aiwatar da yarjejeniyar.

A cewar yarjejeniyar, bangarorin biyu za su yi aiki tare wajen tallafawa tare da raya manufofin kasar na yaki da akidar kaifin ra'ayin addini wanda zai inganta kwazon jami'ai da ci gaba da gudanar da zuzzurfan bincike tare da inganta musayar bayanai da kuma wayar da kai.

An kafa hukumar SNCCT ne a shekarar 2004 da zummar kawar da hadarin tsattsauran ra'ayi a kasar Sudan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China