in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan tace rahoton CIA alamu ne na dage mata dukkan takunkumi
2017-05-15 11:27:44 cri
Gwamnatin Sudan ta sanar a jiya Lahadi cewa, ta yi amanna takunkumin da Amurka ta kakaba mata shekaru 20 da suka gabata za'a dage su baki daya, wannan kuwa na zuwa ne bayan wani rahoto da hukumar leken asiri ta Amurkar (CIA) ta ambata cewa alamu sun gwada cewar kasar Sudan ta cika dukkannin sharudan da suka dace na cire mata takunkumin.

Cibiyar yada labarai ta kasar Sudan (SMC), ta jiyo ministan yada labarai na kasar Ahmed Bilal Osman yana cewa, Sudan ta cika dukkan sharrudan da suka dace, abin da ya fi dacewa shi ne a cire mata takunkumin.

Ya bayyana rahoton na CIA a matsayin "na gaskiya", yana mai cewa kasarsa tana da kyakkyawar fata majalisar dokokin Amurka da kuma shugaban kasar za su dagewa kasar ta Sudan takunkumin.

Ministan ya kuma nuna cewa Khartoum tana yin hadin gwiwa da Amurka daga dukkan fannoni, don haka abu ne mai muhimmanci a dagewa kasar takunkumin.

Tun da farko, gwamnatin Washington, ta gindaya wasu sharruda ga Sudan din wadanda dole ne ta cika su kafin dage mata takunkumin wadanda suka hada da gabatar da rahoto nan da ranar 12 ga watan Yuli dake nuna cewa kasar tana da aniyar yaki da ta'addanci da kuma shirin tsagaita bude wuta a dukkan yankunan dake fama da rikice-rikice a kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China