in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya nemi afuwa game da rashin halartar taron kolin kasashen musulumi da Amurka a Riyadh
2017-05-19 20:06:00 cri
A yau Jumma'a ne shugaba Omar al-Bashir na Sudan ya nemi afuwa game da rashin halartar taron kolin shugabannin kasashen Larabawa musulmi da Amurka wanda za a gudanar da birnin Riyadh na kasar Saudiya.

Kamfanin dillancin labatrai na kasar Sudan SUNA ya ruwaito shugaban na yiwa shugabannin kasashen dake halartar taron fatan alheri da samun nasara. Ya kuma bayyana fatan cewa,taron kolin zai kare muradun bil-Adama tare cimma nasarar manufofin shirya shi.

Tun da farko dai sai da shugaba al-Bashir ya samu sakon goron gayyata daga sarkin Salman bin Abdulaziz na kasar Saudiya ta hannu manzonsa na musamman.

Koda yake, ofishin jakadancin Amurka da ke Khartoumn ya bayyana a ranar Laraba cewa, Amurka ba ta goyon gayyatar duk wanda kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ICC ta mika sammacin kama shi, ciki kuwa har da shugaba al-Bashir na Sudan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China