in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta jinjinawa Sudan bisa kokarinta na saukaka halin jin kai a Sudan ta Kudu
2017-05-29 12:14:31 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta fidda wata sanarwa dake cewa, MDD ta nuna gamsuwa da yadda kasar ke tallafawa makwafciyar ta Sudan ta kudu a fannin bada agajin jin kai.

Sanarwar ta ce, ministan harkokin wajen Sudan ya amshi wani sako a ranar Lahadi daga ofishin babban magatakardar MDD, wanda cikin sa Mr. Antonio Guterres ke jinjinawa mahukuntan Sudan, bisa taimakon jin kai da suke baiwa jama'ar Sudan ta kudu dake cikin matsananciyar bukata.

Kaza lika MDD ta nuna gamsuwa, bisa kofa da Sudan ta bude, wadda ke baiwa sauran masu ruwa da tsaki damar shigar da tallafi zuwa Sudan ta kudu, baya ga karbar 'yan gudun hijirar kasar da Sudan din ke yi.

Mr. Guterres ya kuma ja hankalin kasashe mambobin MDD, da su zage damtse wajen samar da kudaden da ake bukata, don tallafawa 'yan gudun hijirar dake samun mafaka a Sudan, da ma na sauran kasashe makwaftan Sudan ta Kudu. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China