Wannan dan kasar Faransa yana cikin lafiya yayin da yake isa filin jiragen saman birnin Khartoum, kuma ya bayyanawa 'yan jarida a filin jirgin saman cewa, ya nuna godiya ga bangarorin da abin ya shafa da suka yi kokari wajen cetonsa.
Bisa labarin da fadar shugaban kasar Faransa da kafofin watsa labaru na kasar Faransa suka bayar, an ce, wannan dan kasar Faransa ya taba yin aiki a wani kamfanin hakar ma'adinai, an yi garkuwa da shi ne a gabashin kasar Chadi kuma an kai shi zuwa kasar Sudan. (Zainab)