in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi suka game da tsoma bakin kungiyar G7 a harkokin da suka shafi tekun kudanci da na gabashin kasar
2017-05-28 11:48:48 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya soki lamirin kasashe mambobin kungiyar G7, bisa abun da ya kira yunkurinsu na tsoma baki, cikin harkokin da suka shafi tekun kudanci da na gabashin kasar Sin, suna masu fakewa da biyayya ga dokokin kasa da kasa.

Kalaman Mr. Lu dai sun biyo bayan sanarwar bayan taro, wadda kungiyar G7 ta fitar a ranar Asabar, inda cikinta kungiyar ta ce ta damu, game da halin da ake ciki a wadannan sassa na ruwa dake kewayen kasar Sin.

Sanarwar bayan taron ta G7, ta kuma bayyana fatan mambobinta na ci gaba da daukar matakan doka, wajen warware rashin jituwa da ake fama da shi, tsakanin kasashen dake da nasaba da wadannan yankunan ruwa.

Sai dai a nasa bangare Mr. Lu Kang, ya ce matsayin kasar Sin game da yankunan tekun kudanci da na gabashinta a bayyane yake, kuma mataki ne da kasar ba za ta sauya shi ba.

Ya ce Sin ta yi imanin cewa, za a iya kaiwa ga warware takaddama game da batutuwa masu alaka da wadannan yankuna ne kadai, idan kasashe masu ruwa da tsaki a harkar suka hada kai da juna, suka shiga shawarwari kai tsaye, hakan ne kuma zai ba da damar wanzar da zaman lafiya da daidaito a wadannan yankuna.

Daga nan sai Mr. Lu ya yi kira ga kasashen da batun yankunan ya shafa, da su kansu mambobin G7, su maida hankali ga fahimtar ainihin halin da ake ciki, su kaucewa goyon bayan wani sashe ba dalili, tare da martaba kokarin da kasashe masu ruwa da tsaki ke yi a yankunan, maimakon furta kalamai marasa ma'ana. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China