A yayin taron manema labarai na hadin gwiwa da firaminstan kasar Sin Li Keqiang, Mr. Cazeneuve ya bayyana cewa, Faransa na da burin ganin ta yi aiki tare da Sin, a fannin dakile kariyar cinikayya, tare da daukar dukkanin matakan da suka dace na ciyar da kasashen biyu gaba.
Shi ma a nasa tsokaci yayin taron, firaminista Li Keqiang cewa ya yi Sin da Faransa na da kujerun dindindin a kwamitin tsaro na MDD, kuma burin Sin ne ta ga ta bude kofarta ga kowa, kana tana fatan yin mu'amala ba tare da rufa rufa ba, da kuma cimma moriyar juna.
Kaza lika tana adawa da daukar matakai na kariyar cinikayya, yayin da take goyon bayan barin kasuwa ta yi halinta tsakaninta da sauran kasashen duniya.
Har ila yau a cewar Mr. Li, Sin za ta ci gaba da rungumar yarjejeniyoyin bunkasa cinikayya na kasa da kasa, da ma wadanda take kullawa tsakanin ta da wasu sassa. (Saminu Hassan)