Yanzu haka dai Emmanuel Macron ya lashe babban zaben Faransa na bana, bayan ya kada abokiyar takararsa Marine Le Pen. Zai kuma kasance shugaban kasar Faransa na 8 a jamhuriyar kasar ta 5.
Faransa dai ita ce kasar farko a nahiyar Turai da ta kulla huldar diflomasiyya da sabuwar kasar Sin. (Saminu Hassan)