Za dai a shirya kira taron tattaunawa kan "yarjejeniyar hana makaman nukiliya" a birnin New York a ran 27 ga watan nan da muke ciki. Game da hakan ne kuma, a yayin taron manema labaru da aka shirya yau Litinin, da take ba da amsa ga tambaya game da ko kasar Sin za ta halarci wannan taro ko a'a? Hua Chunying ta ce, har kullum bangaren Sin yana mu'amala, da musayar ra'ayoyinsa ba tare da boye kome ba, da dukkanin bangarorin masu ruwa da tsaki.
Ta ce bisa nazarin da aka yi cikin taka tsantsan, bangaren Sin ya tsai da kudurin cewa, ba zai halarci wannan taro ba. Dalilin da ya sa hakan kuwa shi ne, Sin na fatan za a kiyaye ka'idojin jan damara, da rage yawan sojoji, da makamai da ake bi yanzu, tare da fatan gudanar da hakan sannu a hankali. Wannan kuduri ya bayyana yadda kasar Sin ke sauke nauyin da ke bisa wuyansa, na tabbatar da daidaito da kwanciyar hankali tsakanin kasa da kasa. (Sanusi Chen)