in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministocin kasashen Sin da Burtaniya sun yi musayar sakonnin taya murnar cika shekaru 45 da kulla huldar diflomasiya a tsakaninsu
2017-03-14 09:58:24 cri
A jiya Litinin ne firaministan kasar Sin Li Keqiang da takwarar aikinsa ta kasar Burtaniya Madam Theresa May suka yi musayar sakonnin taya murna da fatan alheri game da cika shekaru 45 da kulla huldar diflomasiya a matakin jakadu tsakanin kasasahen biyu.

Firaminista Li ya bayyana a cikin sakonsa cewa, a cikin wadannan shekaru kasashen Sin da Burtaniya sun kara zurfafa hadin gwiwa a fannin kiyaye muradun juna, baya ga tarin nasarori da sassan biyu suka cimma, yayin da musaya tsakanin al'ummominsu da kuma cudanya ta fannin al'adu tsakanin kasashen biyu ta karu.

Mr Li ya kara da cewa, a halin yanzu dangantakar kasashen biyu ta shiga wani muhimmin mataki, kuma dangantakar tasu tana da kyakkyawan ginshiki da yanayin da za ta ci gaba da bunkasa.

A nata jawabin, Madam May ta bayyana cewa, hadin gwiwar Burtaniya da Sin ta karfafu, inda sassan biyu ke kara musayar ra'ayoyi da tuntubar juna da karuwar huldar ciniyayya da zuba jari. Sauran fannomnin sun hada da karuwar musayar al'adu da kuma al'ummomin kasahen biyu wadanda suka taimaka matuka wajen inganta yanayin kasashen biyu. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China