in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ba da gudumawar sama da kashi 70 na yaki da talauci a duniya
2016-12-28 11:07:54 cri

Bayanan alkaluma game da yaki da talauci da aka fitar a jiya Talata sun nuna cewa, adadin al'ummar Sinawa da suka samu nasarar kubuta daga cikin kangin talauci cikin shekaru 30 da suka gabata ya kai sama da kashi 70 cikin 100 na adadin wadanda aka tsame daga kangin fatara a duniya.

Tun a shekarar 1978, kasar Sin ta samu nasarori masu yawan gaske game yaki da fatara.

Daga shekarar 1978 zuwa 2015, yawan al'ummar kasar Sin mazauna yankunan karkara dake rayuwa cikin kangin talauci ya ragu, daga mutane miliyan 770 zuwa mutane miliyan 55.75,

Cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewa ta kasar Sin tare da hadin gwiwar ofishin yaki da fatara da bunkasuwa na majalisar gudanarwar kasar Sin ne suka fitar da bayanan alkaluman.

Bisa ga kididdigar da bankin duniya ya fitar na yadda dan adam zai iya rayuwa a kullum kan dalar Amurka 1.9 (wanda dan adam zai iya biya bukatunsa a rana) a shekarar 2011, yawan masu fama da talauci ya ragu a fadin duniya zuwa mutane biliyan 1.1 a tsakanin shekarun 1981 zuwa 2012.

A cikin wannan wa'adin da aka kebe, kasar Sin ta tsame mutane miliyan 790 daga kangin talauci, wato kaso 71.82 cikin 100 na adadin yawan mutanen masu fama da talauci a duniya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China