in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana da Masar za su hada kai don yakar ta'addanci
2017-05-11 09:52:05 cri

A jiya Laraba kasashen Ghana da Masar suka cimma matsaya game da yin hadin gwiwa don yakar ta'addanci a nahiyar Afrika.

Kasashen biyu sun kuma amince za su budewa juna kofa, domin zuba jari a tsakanin kasashen biyu.

Wannan yarjejeniya ta biyo bayan wata ziyara ce da ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry ya kaiwa takwararsa ta kasar Ghana Shirley Ayorkor Botchway a birni Accra.

Shoukry yana ziyarar aiki ne ta kwanaki biyu a kasar ta yammacin Afrika.

Dukkan bangarorin biyu sun amince za su hada kai domin yakar ta'addanci wanda shi ne babban abin da yake addabar kasashen Afrika kamar yadda Madam Botchway ta ambata.

Shoukry ya ce, yana fata hadin kan Ghana da Masar zai samar da sabon yanayin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.

Ya ce, akwai manyan masu zuba jari daga kasar Masar wadanda za su yi amfani da babbar dama ta zaman lafiya da tsaro a Ghana domin zuba jarinsu.

Kasashen biyu sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi game da zurfafa mu'amalar siyasa da tattaunawa da juna.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China