Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya gana da mambar hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, kuma ministar ma'aikatar hadin kan jam'iyyun kasar wato Sun Chunlan.
Yayin ganawar da ta gudana jiya a fadar shugaban kasar na Masar, Sun Chunlan, ta mika sakon gaisuwa da fatan alherin na shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaba Al-sisi, inda kuma ta yi Allah wadai da harin da aka kai a kasar a farkon makon nan.
Sun Chunlan ta ce, kasar Sin ta na mai da hankali sosai kan huldar dake tsakaninta da Masar, kuma ta na son karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu domin samun ci gaba tare.
A nasa bangare, shugaba Al-Sisi, ya bukaci Sun ta mika wa shugaba Xi gaisuwarsa, kuma ya ce, yana mai jinjinawa nasarorin da kasar Sin ta samu.
Har ila yau, ya bayyana cewa, ya dauki huldar dake tsakanin Masar da Sin da muhimmanci matuka, yana mai fatan kasashen biyu za su kara karfafa hadin gwiwa domin dakile ta'addanci a fadin duniya.(Jamila)