A jiya Litinin ne kasashen Sin da Masar suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna, da za ta bunkasa ayyukan fasahar zamani, da cinikayya, da raya masana'antu a tsakaninsu.
Sakatare janar na kwamitin raya kasa da kwaskwarima na kasar Sin Li Pumin ne ya rattaba hannu a madadin kasar, yayin da ministan harkokin sadarwa da fasahar zamani na kasar Masar, Yaseer Qadi ya rattaba hannu a madadin kasarsa.
Yarjejeniyar na da nufin samar da wani rumbun adana bayanai domin huldar cinikayya da zuba jari ta intanet, tare da karfafa hadin gwiwa a fannin fasahar zamani, ta hanyar amfani da wani sabon tsari mai suna 'Online Silk Road' da zai hada biranen kasar Masar da takwarorinsu na kasar Sin.
Har ila yau, a jiyan, Li Pumin tare da jami'an ma'aikatar kare muhalli ta Masar, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kara bunkasa dangantakar kasashen, kan batutuwa da suka jibanci muhalli.( Fa'iza Mustapha)