in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Masar ya ayyana dokar ta baci ta watanni uku a kasar
2017-04-10 09:41:49 cri

Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah Al-Sisi, a jiya da yamma, ya sanar da ayyana dokar ta baci ta watanni uku a kasar, bayan wasu hare-hare da aka kai kan mujami'u biyu, da suka yi sanadin mutuwar mutane a kalla 44, tare da jikkata 120.

Abdel-Fattah Al-Sisi, wanda ya bayyana haka bayan kammala jagorantar taron majalisar tsaron kasar, ya ce za a dauki matakai, ciki har da ayyana dokar ta baci ta tsawon watanni uku, bayan an kiyaye dukkan ka'idojin shari'a da kundin tsarin mulkin kasar.

Ya kuma sanar da kafa wata majalisar koli kan yaki da akidar ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, da sabuwar doka da za ta ba ta cikakken damar gudanar da aikin.

Tuni dai kungiyar IS ta dauki alhakin kai hare-haren, da ma wanda aka kai kan wata mujami'a a birnin Alkahira cikin watan Disamban bara, wanda ya yi sanadin mutuwar masu ibada 28, wadanda mafiya yawansu mata ne da kananan yara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China