Ministan harkokin cikin gidan Masar ya ce, 'yan sanda sun kashe wanda ya kai hari shingen binciken motoci a kudancin Sinai.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, ministan ya ce, jami'an tsaro sun gano wurin da maharin ya buya, inda kuma suka kashe yayin musayar wuta.
Harin da aka kai ranar Talata kan wani shingen bincike dake kusa da mujami'ar St. Catherine a kudancin Sinai, ya yi sanadin mutuwar 'dan Sanda daya, tare da jikkata wasu guda hudu.
Wannan hari dai ya zo ne bayan kai wasu hare-hare kan mujami'u biyu a farkon makon da ya gabata, da suka yi sanadin rayukan mutane 47, harin da kungiyar IS ta dauki alhakinsa. (Fa'iza Mustapha)