in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin "Ranar Afirka" ta 54 a birnin Beijing
2017-05-26 13:54:37 cri

A jiya Alhamis ne aka gudanar da bikin "Ranar Afirka" a cibiyar diflomasiyya dake birnin Beijing na nan kasar Sin. Shugaban tawagar jadakun kasashen Afirka dake kasar Sin, kana jakadan kasar Madagascar Victor Sikonina, da jakadan kasar Habasha Seyoum Mesfin, da jakadan kasar Guinea Sow Ibrahima Sory, da kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Ming sun halarci bikin, inda suka kuma ba da jawabi.

Ban da haka kuma, ministan harkokin watsa labarai na kasar Guinea wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a nan birnin Beijing, da jakadun kasashen Afirka da masu dakin su, da kuma wasu wakilan bangarori daban daban da yawan su ya haura 500, sun halarci wannan babban biki da aka shirya.

A yayin da yake jawabi, Victor Sikonina ya bayyana cewa, gudanar da bikin "Ranar Afirka" a kasashen duniya yana da muhimmiyar ma'ana, sabo da baya ga matsayin "Ranar Afirka" dake nuna tarihi, haka kuma, bikin na baiwa gamayyar kasashen duniya damar nuna farin ciki na samun 'yancin kai da mutuncin su, kamar yadda yake a kasashen Afirka.

Bugu da kari, ya ce, jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a yayin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa na "Ziri daya hanya daya", ya bude wani sabon shafi ta fuskar kafa sabon tsarin duniya, da kuma kafa dangantakar hadin gwiwa mai adalci, mai cike da zaman lafiya da kuma burin samun dauwamammen ci gaba.

Ya kuma kara da cewa, tabbas kasashen Afirka za su sami ci gaba, sun kuma dauki shawarar "ziri daya hanya daya" a matsayin wani ginshikin ci gaba a fannin hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wanda ka iya samar da dama ga kasashen Afirka, ta ba da gudummawa kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya.

A nasa bangare, Mr. Zhang Ming ya ce, kasar Sin tana maraba da halartar kasashen Afirka shawarar "ziri daya hanya daya" a nan gaba, kuma kasar Sin za ta ci gaba da taimaka wa kasashen Afirka wajen samun dauwamammen ci gaba, bisa manyan shirye-shirye guda goma na hadin gwiwar Sin da Afirka, karkashin ajandar shekarar 2063 ta kasashen Afirka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China