Yayin wannan taro, wasu shugabanni na kasashe daban daban sun yi jawabai, inda shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya ce, matakin da za a iya dauka don daidaita matsalar kwararowar 'yan gudun hijira daga Afirka zuwa Turai shi ne, kyautata sha'anin ilimi, da kara samar da guraben ayyukan yi.
A nasa bangaren, yariman kasar Jordan, Hussein bin Abdullah, ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su taimakawa matasan duniya, musamman ma na gabas ta tsakiya, a kokarinsu na kafa kamfanoni masu zaman kansu.
Yayin da babban sakataren zartaswa na dandalin tattalin arzikin kasa da kasa, Klaus Schwab, ya yi kira ga shugabannin kasashen dake gabas ta tsakiya, da su kara sauraron shawarwarin matasa, kafin su yanke shawara kan wasu harkokin siyasa.(Bello Wang)