A jawabinsa wanda mataimakinsa ya karanta a madadinsa, shugaban hukumar zartarwar kungiyar ta AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana cewa,duk da ci gaban da aka samu a nahiyar tun bayan kafa kungiyar hada kan kasashen na Afirka shekaru 54 da suka gabata, har yanzu nahiyar tana fuskantar tarin kalubaloli.
Shugaban ya ce manyan kalubalolin da nahiyar ke fuskanta sun hada da rage ci gaba karuwar al'umma, kiyaye muhalli da matsalar canjin yanayi, batun kaurar jama'a. Sauran sun hada da rashin aikin yi tsakanin matasa, ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, fataucin mutane, gibi a fannonin siyasa da tsarin tafiyar da mulki, sai kuma batun zaman lafiya da tsaro da sauransu.
Ya nanata cewa, cikin shekaru 15 din da suka gabata, ci gaba nahiyar bai gaza kaso 5 cikin 100 ba, kana akwai kasashe 6 na nahiyar da suke cikin kasashe 10 na farko dake da saurin karuwar tattalin arziki a duniya.
Ya ce, shugabannin kasashen kungiyar AU sun bullo da ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063 a shekara 2015 ne domin tunkarar kalubalen da nahiyar ta ke fuskanta
Shi ma a sakonsa dangane da murnar wannan rana, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, akwai bukatar ajandar da ake fatan cimmawa nan da shekarar 2030 da wadda kungiyar AU ke fatan cimmawa nan da shekarar 2063, su dace da al'ummomin nahiyar ta yadda za su amfana da wadannan matakai.
Ya kuma lura da cewa, kungiyar AU da MDD suna aiki kafada da kafada bisa manufofi 4 na mutunta juna,hadin kai, taimakawa juna da kuma dogaro kan juna.
Abubuwan da aka gudanar yayin bikin wanda ya gudana a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababan kasar Habasha, sun hada da tattaunwa, nune-nunen kayayyakin sakawa wadanda suke nuna al'adu da sauran kayayyakin kasashe mambobin kungiyar. An kuma gudanar da kade-kade da raye-raye da gasar wasanni da sauransu.(Ibrahim)