Mr Guterres ya bayyana hakan ne cikin sakon da ya aika albarkacin ranar Afirka. Yana mai cewa ranar Afirka ta wannan shekara ta zo a kan gabar da nahiyar ke kokarin tabbatar da zaman lafiya,raya tattalin arziki da samun ci gaba mai dorewa.
Jami'in na MDD ya kuma bayyana cewa,kowane bil-Adama zai amfana ta hanyar sauraro da koyo da kuma aiki da al'ummar nahiyar Afirka. Ya ce, duniya na bukatar canjawa daga daidaita rikici zuwa hana aukuwarsa tun farko.
Ya ce, galibin rikice-rikicen da ke faruwa na cikin gida ne, wadanda ke faruwa sakamakon gwagwarmayar neman mulki da albarkatu, nuna bambanci, mayar da wasu saniyar ware, rashin mutunta hakkin bil-Adama da kuma banbancin kabila. Wadanda ake amfani da kaifin kishin Addini wajen ruruta su ko suke ruruta su.
Amma kuma ya ce, batun kare rikice-rikice ya wuce maganar mayar da hankali a kan rikicin kansa.(Ibrahim)