in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daraktan janar na hukumar WHO ya sake jaddada manufar kasar Sin daya tak a duniya
2017-05-25 10:02:07 cri
Jiya Laraba, sabon daraktan janar na hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya sake jaddada cewa hukumar WHO za ta ci gaba da goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma za ta warware matsalar dake shafar yankin Taiwan bisa kudurin babban taron MDD da kudurin babban taron hukumar WHO.

A yayin ganawarsa da shugabar ma'aikatar kula da harkokin kiwon lafiya da shirin kayyade iyali ta kasar Sin Li Bin, a babban taron kiwon lafiya na kasa da kasa karo na 70, Mr. Ghebreyesus ya bayyana cewa, wannan shi ne ganawar da ya yi a tsakanin bangarori biyu karo na farko, bayan ya kama aikin daraktan janar na hukumar WHO, zai ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin hukumar WHO da kasar Sin.

A nata bangare, Li Bin ta ce, kasar Sin tana sa ran zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu bisa fannoni daban daban da abin ya shafa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China