Haka kuma, Ms. Li ta ce, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali kan kiyaye lafiyar al'ummar kasar a ko da yaushe, ta kuma mai da harkar kiwon lafiyar jama'ar kasar a matsayin abu mafi muhimmanci cikin shirin neman bunkasuwar kasar baki daya, shi ya sa, gwamnatin kasar Sin ta kafa wani shirin jinya bisa tushe dake tallafawa al'ummar kasar da yawansu ya kai mutane biliyan 1 da miliyan 300, inda ta kyautata yanayin adalci da kuma inganta aikin jinya, lamarin da ya dace da halin da kasar Sin take ciki, da kuma ba da tabbaci wajen cimma burin neman dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030.
A jiya Litinin ne, aka bude babban taron kiwon lafiya na kasa da kasa karo na 70 a birnin Geneva na kasar Switzerland, inda aka mai da takan taron "kafa shiri mai kyau wanda zai dace da kiyaye lafiyar mutanen kasa da kasa cikin lokaci na neman dauwamemmen ci gaba". (Maryam)