in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zabi Adhanom dan kasar Habasha darakta janar WHO
2017-05-24 09:35:45 cri

Tedros Adhanom, dan shekaru 52, tsohon ministan lafiyan kasar Habasha, kuma tsohon ministan harkokin wajen kasar, an zabe shi a matsayin sabon darakta janar na hukumar lafiya ta duniya WHO.

An zabi Adhanom ne, a lokacin babban taron hukumar lafiyar ta duniya WHO karo na 70 a Geneva, zai maye gurbin Margaret Chan, wadda take rike da mukamin tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2007.

Adhanom ya rike mukamin ministan harkokin wajen Habasha tsakanin shekarar 2012 zuwa 2016, da kuma ministan lafiya tsakanin 2005 zuwa 2012

Ya taba rike hukumar kula da asusun yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta duniya AIDS, da shirin yaki da cutar tarin TB da shirin yaki da cutar Malariya, kuma ya jagoranci shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu da jarirai.

A ranar 1 ga watan Yuli ne Adhanom zai kama aikin jagorancin hukumar na tsawon shekaru 5. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China