in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO: Tasirin muhalli kan lafiyar yara
2017-03-06 13:24:57 cri
A yau Litinin a Geneva, hukumar lafiya ta duniya wato WHO a takaice ta fitar da rahotanni guda biyu game da muhalli da lafiyar yara. Rahotannin sun nuna cewa, a ko wace shekara yara 'yan kasa da shekaru 5, kimanin dubu 1700 ne suka rasa rayukansu sakamakon rashin kyan muhalli. Saboda haka, rahotannin sun yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakai don samar da wata duniya mai dauwamammen ci gaba.

Babbar daraktar WHO madam Margret Chan ta ce, gurbataccen muhalli na iya haddasa mutuwar mutane, musamman ma kananan yara. A lokacin da suke girma, cikin sauki ne, gurbatacciyar iska da ruwa suna iya kawo musu illa.

A sa'i guda kuma, rahotanni sun nuna cewa, wasu dalilan da suke sanya rasuwar yara kananan 'yan wata guda zuwa shekaru 5 da haihuwa su ne zawo, da zazzabin cizon sauro da kuma ciwon huhu, wadanda ake iya rigakafinsu ta hanyar daukar matakan da suka dace.

Baya ga haka, rahotannin sun shawarci hukumomin gwamnati da su hada kai don kyautata muhalli, kamar kara yawan motocin sufurin jama'a, da yankunan da aka dasa itatuwa, hanyoyin da jama'a za su rika tafiya da kuma hawa keke, rage amfani da maganin kashe kwari masu kawo illa ga amfani noma, da rage amfani da sinadarai a fannin masana'antu, da kuma sarrafa shara masu gurbata muhalli yadda ya kamata. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China