Kididdigar MDD ta nuna cewa, jami'an soji da 'yan sanda da fararen hula masu wanzar da zaman lafiya 117, daga kasashe 43 ne suka mutu a bana.
Yayin wani biki da aka kuma a yi a jiyan, an ba jami'an da suka kwanta dama lambar yabo ta Dag Hammarskjold.
Uku daga cikin jami'an 117 'yan kasar Sin ne da suka hada da Sajan Liangliang Shen wanda ya yi aiki karkashin shirin wanzar da zaman lafiya na MINUSMA a Mali, da kuma Kopral Lei Li da Sajan Shupeng Yang wadanda suka yi aiki karkashin shirin UNMISS a kasar Sudan ta Kudu.
A cewar wakilin Sin a MDD Liu Jieyi, jami'an uku sun sadaukar da rayukansu ga shirin wanzar da zaman lafiya, kuma da kwarin gwiwar da ta samu daga gare su, Sin za ta ci gaba da mara baya ga shirin wanzar da zaman lafiya a duniya, ba tare da nuna gazawa ba. (Fa'iza Mustapha)