Patricia Espinosa wadda ta yi wannan kira a jiya Alhamis, yayin sabon zagaye na taron masu ruwa da tsaki a ayyukan UNFCCC, ta ce a wannan zama, za a tattauna ne game da matakan aiwatar da wannan yarjejeniya, tare da gabatar da shiri game da taro na 23 na yarjejeniyar ta Paris, wanda zai gudana a watan Nuwamba mai zuwa a birni Bonn na kasar Jamus.
A daya bangaren kuma Espinosa ta jinjinawa rawar da kasar Sin ke takawa, game da goyon bayan yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, tana mai cewa Sin na taka rawar gani wajen rungumar ayyukan UNFCCC, tare da shiga tattaunawa mai ma'ana da sauran masu ruwa da tsaki.
Ta ce jawabin goyon baya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, yayin taron tattalin arziki na Davos wanda ya gudana cikin watan Janairun farkon wannan shekara, wanda a cikin sa shugaban ya bukaci dukkanin kasashen da suka sanya hannnu kan yarjejeniyar su sauke nauyin dake kan su, ya nuna irin muhimmiyar rawa da Sin ke takawa a wannan fanni.(Saminu Alhassan)