Dujarric ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai a jiya, inda ya ce MDD ta damu da lafiya da tsaron 'yan matan da aka saki da kuma wadanda har yanzu ake ci gaba da garkuwa da su, tana mai kira ga iyalan wadanda aka saki da dukkan al'umar kasar, su karbe su, su kuma ba su kwarin gwiwar sake gudanar da rayuwarsu kamar da.
Dujarric ya kara da cewa, MDD ta yi kira ga kasashen duniya su ci gaba da nuna goyon baya ga gwamnatin Nijeriya don tabbatar da sakin dukkan mutanen da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su tare da sake shigar da su cikin zamantakewar al'umma.
A daren ranar 6 ga watan nan ne, Jami'in gwamnatin Nijeriya ya tabbatar da cewa, an saki 82 daga 'yan matan Sakandaren Chibok da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar. (Zainab)