in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya ce za a ci gaba da yin kwaskwarima kan tsarin MDD
2017-05-06 13:20:59 cri
Kakakin MDD Stéphane Dujarric ya bayyana cewa, babban sakataren Majalisar Antonio Guterres ya mika wasika ga kasashen membobi game da ci gaban da aka samu a fannin yi wa kundin tsarin MDD kwaskwarima.

Stephane Dujarric ya bayyana cewa za a ci gaba da yin kwaskwarimar ne a fannonin kyautata tsari da kiyaye zaman lafiya da sauransu.

Kakakin Majalisar ya ce kasashe sun riga sun cimma wasu yarjejeniyoyi a fannonin samun ci gaba mai dorewa da sauyin yanayi da samar da dawwamamiyar zaman lafiya da tattara kudi don samun ci gaba.

Antonio Guterres na son ci gaba da sa kaimi ga yin kwaskwarimar, ta yadda MDD za ta kara taka rawa wajen cimma burin kasashe membobinta da kuma tunkarar kalubale.

Dujarric ya bayyana cewa, cikin wasikar, Guterres ya bayyana irin ci gaban da aka samu a fannoni da dama da suka hada da samar da daidaito ga mata da kwaskwarima kan tsarin samun ci gaba, da tsarin kiyaye zaman lafiya da tsaro, da sarrafa harkokin MDD, da kafa sabon ofishin yaki da ta'addanci, da tabbatar da kariya ga mutanen da suka kai kara, da kuma yaki da cin zarafin mata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China