Wu Haitao ya bayyana a gun taron kwamitin sulhun MDD game da yaki da cin zarafin mata cewa, ya kamata a magance tare da warware rashin jituwa cikin lumana, da kawar da batun cin zarafin mata tun daga tushe.
Har wa yau ya dace kasa da kasa su tsaya tsayin daka, kan warware manyan batutuwa ta hanyar siyasa, da warware rikice-rikice ta hanyar yin shawarwari, da shiga-tsakani da sauransu cikin lumana.
Wu Haitao ya kara da cewa, kasashen da batun ya shafa, suna da alhakin magance da yaki da batun cin zarafin mata, da tabbatar da tsaron mata da yara a yayin rikici. Har wa yau kasa da kasa ya kamata su girmama ikon mallaka da burin kasashen su, da matakan da kasashen za su dauka bisa yanayin da ake ciki, da samar da gudummawa gare su idan akwai bukata. (Zainab)