Da yake jawabi a birnin Maiduguri, lokacin da yake karbar gudunmuwar kayayyakin gini da abinci daga hukumar kula da 'yan gudun hijira da 'yan ci rani ta kasar, Kashim Shettima, ya ce kwanaki biyu da suka gabata ne mataimakinsa ya dawo daga garuruwan Banki da Bama da Pulka, inda ya je domin kwashe kimanin 'yan gudun hijira 3,682 daga garin Banki zuwa Pulka.
Gwamnan ya bayyana cewa, 'yan tada kayar baya sun lalata gidaje 156,453 a jihar, yana mai cewa adadin shi ne kashi 30 cikin 100 na gidajen jihar.
Ya kuma bayyana jin dadinsa game da yadda sojoji suka karya lagon kungiyar, yana mai yabawa gwamnatin tarayya da rundunonin sojin kasar bisa nasarar da suka samu na durkusar da 'yan tada kayar bayan. (Fa'iza Mustapha)