A wani taron al'umma na musamman da aka gudanar a Abuja, babban birnin kasar a ranar Talata, ministoci 9 da shugaban kasar ya nada sun gabatar da rahotonni game da nasarorin da ma'aikatunsu suka cimma tun bayan da suka shiga ofishinsu.
Ma'aikatar yada laabarai da raya al'adu ta kasar ne ta shirya taron, wanda Lai Muhammed ya jagoranta.
Shugaba Buhari ya samu nasarori masu yawa wajen yaki da rashawa, da maido da tsaro, da kuma kokarin fitar da kasar daga cikin matsin tattalin arziki, kamar yadda ministocin suka bayyana, kana sun jaddada cewa shugaban kasar ba zai sauya aniyarsa ba wajen cika alkawuran da ya dauka wa al'ummar kasar.
Ministan yada labarai da raya al'adun na Najeriyar Lai Mohammed, ya shedawa dandazon jama'ar da suka halarci taron cewa, gwamnatin kasar tana samun sakamako mai kyau a yakin da take yi da rashawa, sabanin yadda wasu ke nuna shakku kan wannan al'amari.
A cewarsa, gwamnatin Najeriyar tana kokarin tsabtace fannin shari'a da kuma aiwatar da shirin farfado da tattalin arzikin kasar da samun bunkasuwa kamar yadda aka tsara.
Mohammed ya ce, kawo yanzu gwamnati mai ci ta cimma nasarori masu yawa wajen shirin farfado da tattalin arziki, da maido da zaman lafiya a fadin kasar, musamman a yankin arewa maso gabashin kasar. (Ahmad)