Da yake yiwa manema labarai karin haske game da hakan a birnin Legas cibiyar kasuwancin kasar, babban darektan hukumar ta NDIC Umaru Ibrahim ya bayyana cewa, a 'yan shekarun baya hukumarsa ta taka muhimmiyar rawa wajen sa-ido da kuma taimakawa bankunan, don tabbatar da cewa, ba su shiga wata matsalar kudi ba.
Ya ce irin wadannan jita-jita da wasu bata gari ke yadawa ta hanyar sakonnin wayoyin salula da kafofin sada zumunta, za su kawo illa ga abokan huldar wadannan bankuna da ma tsarin bankunan kasar baki daya.
Ibrahim ya ce hukumar NDIC tana ci gaba da sanya ido kan kalubalen da bankunan kasar ke fuskanta, ta yadda za a ci gaba da kare muradun masu ajiya a bankuna.
A saboda haka, ya bukaci masu ajiya a bankunan kasar da su kwantar da hankulansu, ganin yadda hukumar da babban bankin kasar wato CBN suka kara tsaurara matakan sa-ido a harkokin bankunan kasar. Yana mai cewa, duk wadanda suka ajiye kudadensu a bankunan dake da lasisi, ko shakka babu kobonsa ba zai bata ba.(Ibrahim)