Babban manajan kamfanin TechPlus Taiwo Oyewole ya shaidawa kamfanin dlillacin labarai na Xinhua cewa, bikin baje kolin zai ba da damar kara fahimtar juna game da yadda fasahohin kere-kere ke biyan bukatun ci gaban da kuma harkokin kasuwanci na zamani.
Kamfanonin da ake sa ran za su halarci bikin sun hada daga Najeriya da Afirka ta kudu, da kasar Sin da Faransa da kuma Amurka. Tun daga ranar 8 ga watan Yulin wannan shekara ne, ake sa ran kamfamin zai fara nuna fasahohi da suka shafi manyan fannoni a sama da runfuna 100. (Ibrahim Yaya)